Hula
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
headgear (en) ![]() |
Fabrication method (en) ![]() | Dinkin hula |
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/2/22/Hat_MET_61.94.20_CP1.jpg/220px-Hat_MET_61.94.20_CP1.jpg)
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/f/f9/2_st_r%C3%B6da_toppluvor%2C_A-B._A_-_Nordiska_museet_-_NM.0026010A_%282%29.jpg/220px-2_st_r%C3%B6da_toppluvor%2C_A-B._A_-_Nordiska_museet_-_NM.0026010A_%282%29.jpg)
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/86/WAVES_Garrison_Cap_%2825326923364%29.jpg/220px-WAVES_Garrison_Cap_%2825326923364%29.jpg)
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/a/ab/Cap_%28AM_1982.16-4%29.jpg/220px-Cap_%28AM_1982.16-4%29.jpg)
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/02/Amsterdam_-_Hats_-_0931.jpg/220px-Amsterdam_-_Hats_-_0931.jpg)
Hula Wata sutura ce da ake sawa a kai. A al'adar Malam Bahaushe sa hula na daya daga cikin cikar kamalar ɗa namiji da sura ta girma. Garuruwan da suka shahara a ɗinkin hula su ne kamar haka, Borno da Katsina da Paki. Hula suna ne na "tilo" jam'i kuma "Huluna". Kuma hula tana da mutukar muhimmanci a wajen mutane, musamman ma a Kasar Hausa, kuma tana nuna cikar kamala "cikar ado a wurin Malam Bahaushe sai da hula".
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/9/9e/WPWP_Face_cap.jpg/220px-WPWP_Face_cap.jpg)
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/f/f1/Custom-Peaked-Cap_NoWatermark.jpg/220px-Custom-Peaked-Cap_NoWatermark.jpg)
Hula dai ta samo asali ne tun a ƙarnin baya, inda mutane musamman ma dattawa suka fi amfani da ita domin sanya ta a kai, hula tana kara nuna mahimmanci ga mutane a wasu ƙabilun inda wasu kuma ke sanya ta domin ado. Hula kala-kala ce kuma a Nijeriya kusan kowane yanki da yadda suke sa hula. Kuma maza su ne aka fi sani da sana'ar ɗinkin hula musamman ƴan Maiduguri.[1] [2]
Ire-iren huluna
[gyara sashe | gyara masomin]![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/04/Hula_Dara.jpg/220px-Hula_Dara.jpg)
Hular Dara
[gyara sashe | gyara masomin]Hula ce ta alfarma wacce mutanen Arewacin Najeriya da wasu al'umma a ƙasashen Afirka ke amfani da ita. Mutane kan sanya Dara domin ƙure ado da kece raini.