Jump to content

Bola Tinubu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bola Tinubu
shugabani ƙasar Najeriya

29 Mayu 2023 -
Muhammadu Buhari
Gwamnan Legas

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Mohammed Buba Marwa - Babatunde Fashola
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Rayuwa
Cikakken suna Bola Ahmed Tinubu
Haihuwa Lagos,, 29 ga Maris, 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yaren Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Mahaifiya Abibatu Mogaji
Abokiyar zama Oluremi Tinubu
Karatu
Makaranta Chicago State University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a accountant (en) Fassara, ɗan siyasa da shugabani ƙasar Najeriya
Employers Arthur Andersen (en) Fassara
GTE (en) Fassara
Deloitte (en) Fassara
Mobil Producing Nigeria (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Alliance for Democracy (en) Fassara
Action Congress of Nigeria
All Progressives Congress
Dr Adekunle olayinka with president bola Ahmed tinubu
Asiwaju bola Ahmed tinubu
Bola Tinubu Da Foreign Secretary James Cleverly
Bola Ahmed Tinubu Science Complex, Faculty of Science, Lagos State University.jpg
shugaban kasa

Bola Ahmed Adekunle Tinubu an haife shi a ranar 29 ga watan Maris a shekara ta alif dubu ɗaya da Ɗari Tara da hamsin da biyu (1952) Miladiyya. Bola Ahmed Adekunle Tinubu ya kasance kwararren ɗan siyasar Najeriya, kuma shugaban ƙasar Najeriya tun daga ranar 29 ga watan mayun shekara ta 2023.[1] Ya yi aiki a matsayin Gwamnan jihar Legas daga shekarata alif dubu ɗaya da Ɗari Tara da casa'in da Tara (1999) zuwa shekarata dubu biyu da bakwai (2007), haka yayi Sanata mai wakiltar Legas ta yamma na wani gajeren lokaci a jamhuriya ta uku (Third republic).[2]

Bola Ahmed Tinubu shahararran ɗan siyasa ne a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a kasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya baki daya.

Ana kallon Asiwaju a matsayin wanda ya dade yana jan zarensa tun daga dawowar Najeriya kan mulkin demokaradiyya ta alif dubu daya da dari Tara da casa'in da Tara (1999), Tinubu ya kasance a matsayin uba a fagen siyasa sakamakon karfin fada a ji da yake da shi a siyasar kasar ta Yarbawa da ma Najeriya baki daya.

Haka kuma ya kafa mutane da dama a Najeriya inda ya yi musu hanya suka samu mukamai a tarayya da jihohi. Ihayatu ( talk) 21:37, a ranar 30 ga watan Mayu shekarata 2023 (UTC)) [3][4][5]

Tarihin Rayuwar Tinubu

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Jihar Legas, cikin iyalin Tinubu da suka yi fice a jihar ta legas a ranar 29 ga watan Maris shekarar alif dubu ɗaya da ɗari Tara da hamsin da biyu(1952). Ya halarci makarantar firamare ta St. John's da ke Aroloya da makarantar Children's Home a Ibadan, da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Daga nan sai ya wuce Kwalejin Richard Daley a Birnin Chicago da ke ƙasar Amurka, bayan samun gurbin yin karatu a Kwalejin. Daga baya ya zarce zuwa Jami'ar jihar Chicago, a Illinois inda ya kammala ya kuma fito da Digiri a Harkokin Kasuwanci. Tinubu ya kuma samu kyautar dalibi da yafi kwazo a Jami'ar da kuma shaidar karramawa a ɓangaren Akanta da Hada-Hadar kudi. Da zuwansa Amurka a shekarar 1975, da taimakon mahaifiyarsa, matashin mai hazaka, da kuma ke da himmar ganin ya cimma burinsa. Ya shiga yin ayyuka da za su kawo masa kudi kamar wanke tukwane a gidajen sayar da abinci da aikin gadi da kuma tuka motar-haya domin taimaka masa a bangaren karatunsa. Baiwar da yake da ita ce ta sa ya shiga jerin dalibai masu hazaka na Kwalejin Richard Daley da kuma ta kai har ya kammala karatu a Jami'ar jihar Chicago a shekarar alif 1979, inda ya fito da digiri a bangaren Kasuwanci.

A shekararsa ta farko a Jami'ar Chicago, an karrama shi da mukamin malami mai taimakawa (tutor), domin taimakon wasu 'yan uwansa dalibai da ke wadannan ajuzuwa.

Yan uwansa dalibai da dama sun yaba taimakonsa a bangaren karatunsu wanda har ta kai su ga samun sakamako mai kyau.

A tsawon shekaru da ya yi a jami'a, Tinubu ya kasance dalibi mafi hazaka wanda ya yi ta samun kyautar dalibi mai gwazo da kuma shaidar karatu a bangaren Akanta da hada-hadar kuɗi, inda kuma ya kare digirinsa da sakamako mai daraja ta sama.

A matsayinsa na mai hankoron abubuwa masu kyau da za su zo, Bola ya tsaya tare da yin nasara a takarar shugaban ɗaliban nazarin Akanta da Hada-hadar kuɗi na jami'ar jihar Chicago a shekarar sa ta karshe.[6][7][8]

Asiwaju Bola Tinubu yana da mata ɗaya mai suna Oluremi Tinubu, wadda sanata ce mai wakiltar Jihar Legas ta tsakiya.

Ta kasance mai fafutikar kare Hakkin jama'a da kuma mai ilimi da ake mutuntawa.

Tana kuma gudanar da ayyukan jinkai wanda aka karrama da lambar girmamawa ta kasa ta Officer of the Order of the Niger (OON).

Suna da 'ya'ya da kuma jikoki.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Aiki da kasuwanci

[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin kammala karatunsa na digiri, Bola Tinubu ya samu aiki da kamfanin harkar akantanci na Arthur Anderson. Daga bisani kamfanin Deloitte Haskins (wanda ake kira da deloitte Haskins and Touche a yanzu) suka ɗauki hayarsa, bayan nan kuma sai ya yi aiki da GTE Service Corporation, wani babban kamfanin sadarwa a ƙasar Amurka. A kamfanin Deloitte Haskins and sells, matashi kuma kwararre Bola ya fadada kwarewarsa ta hanyar shiga ayyukan dubawa da gudanarwa na General Motors da yin aiki a Babban Bankin Kasa na Chicago da kamfanin Procter and Gamble da International Harvester da General Electric da sauran kamfanoni. Bayan ganin kwarewarsa, kamfanin Deloitte sal ya dauki hayar Bola a matsayin jagoran mambobi da ke sa ido a kamfanin.[9][10][11]

Dawowarsa Najeriya

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan dawowarsa Najeriya da kuma samun gogewa a ɓangaren hada-hadar kuɗi, Tinubu ya fara aiki da Kamfanin Mai na Mobil a matsayin babban mai bincike wanda ta kai har ya zama ma'ajin kamfanin.

A matsayinsa na mutumin da ba ya manta mafararsa da kuma alakarsa da al'umma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kasance mutumin da ya dauki hidimtiwa al'umma da muhimmanci. Ko da a Mobil, ya jagoranci hada-hada daban-daban na tara-kudi domin tallafa wa shirye-shiryen ci-gaban al'umma a Jihar Legas. Ya kuma jagoranci kungiyar Primrose, wata kungiyar siyasa da ke hankoron kawo canji a siyasar Jihar Lagos. Haka nan, Bola Tinubu ya yanke shawarar shiga aikin hidimar al'umma gadan-gadan ta hanyar ajiye babban matsayi da yake da shi a kamfanin Mobil.

Fara Harkokin Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]
Tinubu a shekarar 2011

Shigarsa ta farko fagen siyasa, ya fara ne da shiga sahu wajen kafa jam'iyyar SDP da shi. A shekarar 1992, aka zaɓe shi a matsayin Sanata da ke wakiltar Yammacin Jihar Legas. A Majalisar Dattijai, ya samu nasarar zama shugaban kwamitin da ke kula da bankuna, kuɗi da kasafi na Majalisar Dattawa wanda babban kwamiti ne na Majalisar Dattawan Najeriya. Bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na ran 12 ga watan Yunin, 1993 da Gwamnatin Mulkin Soja Ta IBB tayi da kuma kara wa'adin mulkin soja, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya Shiga sahun gaba cikin wadanda suka kafa kungiyar masu rajin kare dimokradiyya da aka fi sani da NADECO.

Tinubu tare da Sarki Oba Saheed Ademola da Sarki Elegushi a Shekarar 2017.

Sun tunkari gwamnatin mulkin soji na wancan lokaci wajen ganin an dawo da tsarin dimokuradiyya a Najeriya. Bola Tinubu ya sha barazana ga rayuwarsa da musgunawa wanda har ta kai ga kamawa tare da tsare shi wanda hakan ya sa ya gudu ya bar kasar. Duk da haka bai karaya ba a gwagwarmayarsu ta neman tsarin dimokradiyya inda ya zama shugaban kungiyar ta NADECO da ke gudun hijira, inda ya ci gaba da hankoron ganin mulkin dimokradiyya da tsarin shugabanci a Najeriya. Neman da kungiyar NADECO ke yi daga baya ta sami yin nasara. Yayin da mulkin soja yazo karshe, Bola Tinubu ya dawo Najeriya a shekarar 1998, domin shiga sahun gaba na kawo cigaba da fahimtar juna. Tinubu ya shiga sahun mutane da suka kafa jam'iyar siyasa mai son ci gaba ta Alliance for Democracy (AD), inda ya samu nasarar zamantowa mai yi wa jam'iyyar takarar kujerar gwamna a jihar Legas.

Zama Gwamnan Legas

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan samun nasarar zama gwamnan Jihar Legas a zabukan 1999, Tinubu ya jagoranci jihar har na tsawon shekara 8.

Bayan shigar sa ofis a watan Mayun 1999, Bola Tinubu ya jawo hazikan mutane a cikin gwamnatinsa, wanda tare suka tsara kyakkyawan shiri na shugabancin Jihar lagos.

Ajanda 10 da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai sun kunshi ɓangaren ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da rage talauci, da samar da wutar lantarki da ruwan sha da tsarin zirga-zirga mai kyau da kula da muhalli da doka-da-oda da samar da abinci da kuma farfado da ɓangaren aikin gwamnati.

Bola Ahmed Tinubu a matsayin Gwamnan Lagos a shekarar 2007

Gwamnatin Tinubu, ta inganta tare da gyara tsarin mulki ta hanyar kirkiro da sabbin ma'aikatu irinsu ma'aikatar gidaje da ma'aikatar wasanni da ci gaban matasa da kuma ta harkokin mata da rage talauci.

A tsawon mulkinsa, Asiwaju Tinubu ya kawo hazikai da kuma kwararru a cikin gwamnatinsa a matsayin kwamishinoni da kuma masu ba shi shawara a bangarori da suka kware.

Ta hanyar tsare-tsare da aiwatarwa, gwamnatin Asiwaju Tinubu ta kara kasafin kudin Jihar Legas daga naira biliyan 14.200 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 240.866 a shekarar 2007 domin Jihar ta samar da karin ababen more rayuwa ga al'ummarta.

Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kiyaye rabon kasafin kudi na shekara da akalla kashi 60-40 bisa dari a kan kudin da ake kashewa na manyan ayyuka don tabbatar da an samar da ababen more rayuwa ga al'umma.

Asiwaju Tinubu, ta hanyar kirkire-kirkire da sabbin tsare-tsare ya cire Jihar Lagos daga samun kudaden shiga na shekara-shekara na Naira biliyan 14.64 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 60.31 a shekarar 2006. Ya zuwa watan Maris din 2007, jihar ta samu kudin haraji a wata da ya kai naira biliyan 8.2.

Wannan gagarumin kokari da gwamnatinsa ta samu a jihar Lagos ya biyo bayan bijiro da tsare-tsare da kuma aiwatar wa kamar kirkiro da tsarin bankin laturoni da tsarin sa ido a kudaden da ake tarawa da kaddamar da tsarin a na'ura mai kwakwalwa.

Sannan akwai tsarin biyan haraji na laturoni da sake tsara gudanar da ma'aikatar kula da kudaden haraji na jihar da sake fasalta tsarin karbar kuɗin haraji da samar da bayanan masu biyan haraji.

Jihar Legas karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta zama abin koyi a bangaren tafiyar da aikin gwamnati da kirkire-kirkire da harkokin kudi.

A watan Satumban, 2002, Legas ta kasance jiha ta farko a Najeriya da ta tara kudaden shiga masu yawa don bunkasa ababen more rayuwa. Jihar ta samu kudade ta hanyar karbo takardun lamuni domin aiwatar da ayyukan ci gaba kamar gyara hanyoyi da gina rukunin gidajen milenia da gina harkokin samar da ruwa da gyara kotuna da samar da wuraren zubar da shara da gina azuzuwa da sauran su. Jajircewar Tinubu da taimakon baiwar sa ta siyasa, Bola Tinubu ya hangi barazanar magudin zabe a 2003 daga Jam'iyyar PDP mai Mulki, inda abokansa a yankin kudu-maso-yamma suka saduda da kin yin kamfe na sake zabarsu, amma Tinubu ya bijiro da wani yakin neman zabe mai ma'ana kan irin nasarori da ya samu.

Sauran gwamnonin Jam'iyar AD a jihohin Ondo da Osun da Ekiti da Ogun da kuma Oyo dukkansu sun gamu da cikas wajen sake zabarsu a shekarar 2003, a inda jam'iyyar PDP ta samu nasara. Bola Tinubu ya kasance mutum daya tilo da ya samu nasara a karkashin jam'iyar AD. Da irin nasarorin da ya samu a shugabancin Jihar Lagos, ya samu nasarar kalubalantar gwamnatin tarayya ta fuskar siyasa da kuma shari'a. Saboda jajircewarsa a wannan lokaci, Bola Tinubu ya kasance mutum daya tilo da ya tsaya tsayin daka wajen hana Najeriya zama kasa mai tsarin jam'iyya daya.Ya kasance gwamnan jam'iyyar AD daya tilo a cikin jihohi 36 na Najeriya. Duk da haka, bai karaya ba, inda ya shiga sahun gaba wajen karfafa 'yan siyasa da ke son ci gaba.

A 2007, 'yan siyasar da ke son ci gaba a kudu-maso-yammacin Najeriya suka dawo da martabarsu.

Don sake zama babban dan siyasa na bangaren adawa, Bola Tinubu ya taka rawa wajen kirkiro da sabuwar jam'iyar ci gaba mai suna Action Congress (AC), wadda daga baya ta koma Action Congress of Najeriya (ACN).

Jajircewar Tinubu ce ta kare Jihar Legas daga mamayar Jam'iyyar PDP, sai dai tsarin da ya bullo da shi ya taimaka masa wajen sake farfado da akidar siyasa wanda daga baya ya dawo da ci gaban shugabanci a fadin kudu maso yamma da kuma Jihar Edo.

Idan za a rubuta tarihin wannan lokaci, Tinubu zai kasance a matsayin mutumin da ya tsaya tsayin daka wajen kawo tsarin siyasar ci gaba a yankin kudu-maso-yamma da kuma Najeriya.

Za a san shi a matsayin mutumin da ya jajirce wajen hana jam'iyar PDP cimma burinta na gudanar da tsarin jam'iyya daya a kusa. Wadanda suke da ra'ayin mulkin dimokuradiyya a Najeriya, tilas ne su jinjina gudummawar da Asiwaju Tinubu ya bayar.

Kafa jam'iyyar APC

[gyara sashe | gyara masomin]

A zaɓen 2015, Asiwaju ya zama babban mai goyon bayan hadewar jam'iyyarsa da wasu jam'iyyun adawa biyu Jam'iyyar CPC da kuma Jam'iyar ANPP domin kawo ƙarshen mulkin Jam'iyar PDP.

Jam'iyyun guda uku sun haɗe daga baya inda suka samar da jam'iyar All Progressive Congress (APC).

Duba da rawa da ya taka wajen kafa jam'iyyar, an bai wa Tinubu mukamin jagoran jam'iyyar na kasa.

A nan ma, ya sadaukar da burinsa na siyasa, domin karfafa jam'iyyar da ba ta fifiko a kasa baki daya.

A shekarar 2015, jam'iyyar ta APC ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2015, wanda karon farko da jam'iyyar adawa ta kada shugaba mai mulki a Najeriya. Tinubu ya taimaka wa Jam'iyyar ta APC wajen samun nasara.

Takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC

[gyara sashe | gyara masomin]

A Ranar 22 Ga Watan Yuni Na Shekarar 2022, Bola Tinubu Yayi Sa'ar samun Tikitin takarar a Jam’iyyarsa Ta APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar ce da kuri'u dubu 1271 da masu zaɓe sama da dubu 2300 suka kwashe dare suna kadawa. Tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi ya zo na biyu da kuri'u 316, sai Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo a matsayi na uku da kuri'u 235 sai kuma shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan da ya samu kuri'u 152.

'Yan takara 14 da suka fafata a zaɓen sun haɗa da Mista Chukwuemeka Nwajuba, Fasto Tunde Bakare, Mista Ahmed Rufa’i, Sanata Rochas Okorocha, Mista Jack Rich, Gwamna Ben Ayade, Gwamna David Umuahi, Asiwaju Bola Tinubu, Sen. Ahmed Yarima, Dr Ahmed Lawal, mataimakinsa. -Shugaban kasa Yemi Osinbajo, Mista Rotimi Amaechi, Gwamna Yahaya Bello da Mista Ogbonnaya Onu.

Lashe Zaben Shekarar 2023

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 1 ga Watan Maris 2023, Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023, da kuri'a miliyan 8,794,726.

Fayil:Dr. Adekunle Olayinka with President Bola Ahmed Tinubu GCFR as presidential-elect.jpg
Shugaba Tinubu Tare da Dr. Adekunle Olayinka bayan cin Nasarar Zaben Shugaban Kasa na 2023.

Tsohon matainmakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ne ke biye masa da kuri'u miliyan 6,984,520. Sai kuma ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi wanda ya samu kuri'a miliyan 6,101,533. Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya zo na huɗu da kuri'u miliyan 1,496,687. Amma Sai Dai Jam'iyyun adawa na PDP da LP sun ce ba za su karbi sakamakon ba bisa zargin tafka magudi a mazabu da dama, inda kuma suka ce za su garzaya kotu. An Rantsar da Ahmed Bola Tinubu a Ranar Litinin Ashirin da tare ga watan Mayu a Shekara ta Dubu biyu da a Shirin da Ukku.

  1. https://en.m.wikipedia.org/wiki/Bola_Tinubu
  2. https://punchng.com/tinubu-returns-today-may-present-ministerial-list-after-sallah/
  3. Ewepu, Gabriel (25 October 2019). "CSOs calls on EFCC to investigate Tinubu over alleged money conveyed in bullion vans". Vanguard. Retrieved 22 February 2022.
  4. Olu, Tayo (29 July 2020). "Petition Details Alleged Corrupt Activities Of Tinubu Since 1999". The Whistler. Retrieved 22 February 2022.
  5. Kperogi, Farooq (29 January 2022). "Clarity On Tinubu's Age And Post-Secondary Education". Nigerian Tribune. Retrieved 22 February 2022.
  6. "2023: Controversy Trails Tinubu's INEC Filings". Daily Trust. 26 June 2022. Retrieved 26 June 2022.
  7. Essien, Hillary (24 June 2022). "I didn't attend primary, secondary schools; my university certificates stolen by unknown soldiers, Tinubu tells INEC". Peoples Gazette. Retrieved 1 July 2022.
  8. Abidoye, Bisi. "PT State of the Race: Tinubu's "lost" certificates and Wike's message to Atiku". Premium Times. Retrieved 1 July 2022.
  9. Clowes, William (22 June 2022). "Graft Allegations Dog Nigeria's Main Presidential Hopefuls". Bloomberg News. Retrieved 23 June 2022.
  10. Hundeyin, David (13 July 2022). "Bola Ahmed Tinubu: From Drug Lord To Presidential Candidate". West Africa Weekly. Retrieved 13 July 2022.
  11. Weiss, Michael (27 April 2015). "Nigerian Pres' Svengali Tied to Heroin". The Daily Beast. Retrieved 13 July 2022.