Jump to content

Jigawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jigawa


Wuri
Map
 12°00′N 9°45′E / 12°N 9.75°E / 12; 9.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Dutse
Yawan mutane
Faɗi 6,000,163 (2016)
• Yawan mutane 259.14 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 23,154 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi jihar Kano
Ƙirƙira 27 ga Augusta, 1991
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar zartaswa ta Jihar Jigawa
Gangar majalisa Zauren majalisar dokokin jihar Jigawa
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 720001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-JI
Wasu abun

Yanar gizo jigawastate.gov.ng
Jigawa garin dutse
Bikin al'adar Fulani na Shadi (Soro) a garin Kantoga
Rimgim gate
gidan gwamnatin jihar jigawa
Jigawa dusti

Jigawa Jiha ce dake Arewa maso Yammacin Tarayyar Najeriya. An kafa jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991[1] daga jihar Kano a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Babban birnin jihar shi ne Dutse.[2] Jigawa ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da jihar Yobe a arewa maso gabas, Bauchi a kudu maso gabas da kudu, Kano a kudu maso yamma da kuma Katsina a arewa maso yamma.

Tattalin Arziki

[gyara sashe | gyara masomin]

Tattalin Arzikin Jihar Jigawa yana da alaƙa da ayyukan bangaranci na yau da kullum tare da aikin noma a matsayin babban aikin tattalin arziki. Fiye da kashi 80% na al'ummar jihar sun tsunduma cikin noma da kuma kiwon dabbobi. Ana gudanar da ciniki da kasuwanci na kanana da matsakaita, musamman a harkar noma, kiwo da sauran kayayyakin masarufi. Jigawa ta shahara a fannin Noma da kiwo, Manyan amfanin gona na jihar sun haɗa da gyada, dawa, gero, shinkafa, Ridi, da kuma Zobo (yakuwa).a fannin kiwo kuma, Kiwon shanu, awaki, da tumaki ya yaɗu sosai a jihar.

Fadin Kasa da yawan Jama'a

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Jigawa Tana da fadin ƙasa kimanin muraba'in kilomita dubu ashirin da uku, da ɗari da hamsin da huɗu (23,154) da yawan jama’a kimanin miliyan biyu da dubu ɗari takwas da ashirin da tara da ɗari tara da ashirin da tara (kidayar yawan jama'a shekara ta 1991). Babban birnin jihar shi ne Birnin Dutse.

Fadar masarautar hadejiya

Jihar Jigawa tana da iyaka da jihohi hudu dake Najeriya, su ne: jahar Bauchi, jahar Kano, jahar Katsina,da kuma Yobe. [3] [4].

Yaren Jigawa shine, Hausa

Jigawa wani sassa ne na kasar , a Arewa maso yammacin Nigeria .Hausa hausawa sune mafi rinjaye a jihar Jigawa sannan akwai Fulani [5]da Mangawa da Badawa da Ngizimawa wadanda yarukan kanuri ne. Mafiyawancin su suna a kananan hukumomin Birniwa, Guri da Kiri kasamma.

.Hadeja.[6]

Hadeja jahar jigawa

.

Tsarin masarautar gargajiya a Jihar ya kasu zuwa masarautu guda biyar kowacce tana da basaraken gargajiya mai suna sarki (sarki) da yake gudanarwa tare da Hakimai da dagatai da masu unguwanni suna taimaka musu. Sarakuna da Hakimai, ba kamar sauran masu rike da madafun iko ba, ba sa gudanar da harkokin siyasa, sai dai a matsayin masu kula da al’adu da masu ba gwamnati shawara kan harkokin gargajiya da na addini. Duk sarakunan masu rike da mukamai ne ajin farko.

  • MASARAUTAR HADEJIA[7]
  • MASARAUTAR GUMEL
  • MASARAUTAR DUTSE
  • MASARAUTAR RIGIM
  • MASARAUTAR KAZAURE

https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Jigawa_State.

SHUWAGA BANNIN GANANON HUKUMOMIN JIHAR JIGAWA.

[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan jerin sunayen dake gasa, shine jerin sunayena Shuwaga bannin Gananon Hukumomi guda ashirin da bakwai (27) dake a Jihar Jigawa a wannan shekara ta alif dubu biyu da ishirin da hudu (2024.)

  • Hon. Baffa Shine, Shugan Garamar Hukumar Auyo.
  • Hon. Lawan Ismail Shugan Garamar Hukumar Babura
  • Hon. Umar Baffa Shugan Garamar Hukumar Birni wa
  • Hon. Magani Yusif GigoShugan Garamar Hukumar Birnin Kudu
  • Hon. Abdullahi Sule YariShugan Garamar Hukumar Buji
  • Hon. Bala Usman Shamo Shugan Garamar Hukumar Duste
  • Hon. Sani Muktar Madaka Shugan Garamar Hukumar Garawa
  • Hon. Alh. Mudassir Musa Shugan Garamar Hukumar Garki
  • Hon. Ahmad Rufai Gomel Shugan Garamar Hukumar Gumel
  • Hon. Musa shuaibu Guri Shugan Garamar Hukumar Guri
  • Hon.Zahradden Abubakar Shugan Garamar Hukumar Gwaram
  • Hon. Saleh Ahmad Zauma Shugan Garamar Hukumar Gwiwa
  • Hon. Abdullahi Bala Umar (TO)Shugan Garamar Hukumar Hadejia
  • Hon. Adu Mai unguwa Aujara Shugan Garamar Hukumar Jahun
  • Hon. Muhammad Saminu Yahaya Shugan Garamar Hukumar Kafin Hausa
  • Hon. Alh, Idris Mati Haruna Shugan Garamar Hukumar Kaugama
  • Hon. Arc Muhammad Muktar (mni) Shugan Garamar Hukumar Kazaure
  • Hon. Alhaji Isah Matara Shugan Garamar Hukumar Kiri kasama
  • Hon. Nasiru Ahmad Kiyawa Shugan Garamar Hukumar Kiyawa
  • Hon. Alh, Uzairu Na Dabo Shugan Garamar Hukumar Mai gatari.
  • Shugan Garamar Hukumar Mai gatari
  • Hon. Alhj, Usain Umar Shugan Garamar Hukumar Malam Madori
  • Hon. Adamu Sarki Miga Shugan Garamar Hukumar Miga
  • Hon. Alh, Shehu Suke Ido Shugan Garamar Hukumar Ringim
  • Hon. Alh, Tukur Muhammad Ali Shugan Garamar Hukumar Roni
  • Hon. Saleh Ahmad Dan zumo Shugan Garamar Hukumar Sule Tankarkar
  • Hon. Baffa Yahaya Taura Shugan Garamar Hukumar Taura
  • Hon. Alh, Mubarak Ahmad Shugan Garamar Hukumar yan kwashi.[8]

Ƙananan Hukumomin jihar Jigawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Jigawa tana da ƙananan Hukumomi guda ashirin da bakwai (27). Kananan Hukumomin kuwa su ne:

Ma'adanai da ake samu sun hada da;

  • Laka
  • Bello, Ahmadu, Sir, a shekara ta 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila, Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
  1. Jigawa State - Wikipedia
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://gazettengr.com/nuc-accredits-10-programmes-at-federal-university-dutse/&ved=2ahUKEwiyr4ajwPCGAxW8QUEAHSHFC9kQxfQBKAB6BAgIEAI&usg=AOvVaw0P98KYz8m_E8H_1DZLQ5IO
  3. https://www.britannica.com/place/Jigawa
  4. https://www.familysearch.org/wiki/en/Jigawa_State,_Nigeria_Genealogy
  5. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://guardian.ng/the-gulf-between-fulani-rulers-and-herders/&ved=2ahUKEwiQz-X5wPCGAxXBQkEAHULqNw8QxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw3_dt1-fWHaREhMjJURdWVA
  6. "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 2020-01-10.
  7. https://hausa.leadership.ng/tarihin-hadejia-da-sarakunanta-6/
  8. https://www.jigawastate.gov.ng/2chairmen
  9. https://en.wikipedia.org/wiki/Gumel


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

/gallery>

  • Bello, Ahmadu, Sir, a shekara ta 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila, Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.