Jump to content

James Semple

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
James Semple
Ɗan majalisar Dattawan Taraiyar Amurka

4 ga Maris, 1845 - 4 ga Maris, 1847 - Stephen A. Douglas (mul) Fassara
District: Illinois Class 2 senate seat (en) Fassara
Ɗan majalisar Dattawan Taraiyar Amurka

16 ga Augusta, 1843 - 4 ga Maris, 1845
Samuel McRoberts (mul) Fassara
District: Illinois Class 2 senate seat (en) Fassara
member of the Illinois House of Representatives (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Gundumar Green, Kentucky, 5 ga Janairu, 1798
ƙasa Tarayyar Amurka
Mutuwa Elsah (en) Fassara, 20 Disamba 1866
Makwanci Bellefontaine Cemetery (en) Fassara
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, mai shari'a, Lauya da Mai wanzar da zaman lafiya
Wurin aiki Washington, D.C.
Imani
Jam'iyar siyasa Democratic Party (en) Fassara
James Semple
James Semple

James Semple (Junairu 5, 1798 – Disemba 20, 1866) ya kasance Kakakin Majalisar Wakilan Illinois, Babban Lauyan Illinois, Mataimakin Alkalin Kotun Koli na Illinois, Chargé d'Affaires na New Granada, sannan kuma Sanatan Amurka daga Illinois.[1]

An haifi Semple a Gundumar Green, Kentucky, kuma ya girma kuma ya yi karatu a gundumar Clinton. Ya yi aiki a cikin 'yan bindigar Kentucky a lokacin yakin 1812 sannan ya koma Missouri, inda yake aiki a cikin 'yan bindigar kuma ya mallaki ya kuma gudanar da kasuwanci da dama. Daga baya ya karanci shari'a a Missouri da Kentucky, ya samu zama lauya, sannan ya koma Edwardsville, Illinois, don fara aiki. Ya shiga siyasa a matsayin dan dimukradiyya, amma ya yi adawa da bautar bayi, kuma ya yi aiki a Majalisar Wakilai ta Illinois daga 1828 zuwa 1832. Ya ci gaba da aikin soja bayan ya koma Illinois, kuma ya gwabza a yakin Black Hawk. Bayan aiki a matsayin Babban Mai Shari'a na Illinois daga 1832 zuwa 1834, Semple ya koma gida Illinois, inda ya yi aiki a matsayin Kakakin Majalisa daga 1834 zuwa 1837.

An haifi James Semple a Gundumar Green County, Kentucky, a ranar 5 ga Janairu, 1798, ɗa ne ga John Walker Semple da Lucy (Robertson) Semple.[2] Kakan Semple Robert Semple yayi aiki a majalisar dokokin Virginia, kuma mahaifinsa yayi aiki a majalisar dokokin Kentucky.[2] James Semple ya girma ne a gidan mahaifinsa na Clinton County, wanda John Sample ya sanya masa suna "76".[2] Ya sami ilimin farko daga mahaifiyarsa, mace mai hazaka wacce ta ke da isassheen ilimi da zata yi jayayya ga kararraki a kotu lokacin da babu lauyoyi, kuma kawunsa Isaac Robertson ya koyar da shi, wanda ya kasance mamallakin digiri ne daga Kwalejin Princeton.[2]

A shekarar 1814, Semple mai shekaru goma sha shida ya ba da kansa ga Sojojin Kentucky a lokacin Yaƙin 1812.[2] Ya yi aiki har zuwa karshen yakin, kuma a cikin 1817 ya sami aiki a cikin Rundunar Sojoji na 81st na Kentucky.[2]

A cikin 1818, Semple ya koma Edwardsville, Illinois, amma ya zauna na watanni tara kawai kafin ya koma Kentucky. A cikin 1819, ya yi ƙaura zuwa Chariton, Missouri, inda ya yi aikin masana'antar fatu kuma ya zama mai himma a wasu harkokin kasuwanci.[2] Bugu da kari, ya shiga Rundunar Sojojin Yaki na Missouri ta 21, wanda daga baya ya zama mai ba da umarni da mukamin Kanal. Ba da daɗewa ba bayan ya isa Chariton, an zaɓi Semple a matsayin Kwamishinan Lamuni na jiha.[2] Dangane da firgici na 1819, gwamnatin Missouri ta ba da izinin ba da kuɗin takarda da za a iya ba da rance ga manoma don kada su yi asarar ƙasarsu yayin tabarbarewar tattalin arziki.[3] Kwamishinoni ke kula da Bankunan da ke bada rance a duk fadin jihar, suna bada rance kuma su tabbata an biya su, sannan suka kafa tsarin ba da rance da kuma gwanjon kayan aiki ga manoman da suka kasa cin bashi.[3]

Bayan mutuwar matarsa ​​ta farko a cikin 1821, Semple ya yanke shawarar yin aiki a matsayin lauya kuma ya fara nazarin shari'a.[2] Ya koma Louisville, Kentucky, a cikin 1824 don ci gaba da karatunsa, kuma bayan shekaru uku na karatu an bashi matsayin lauya kuma ya koma Edwardsville a 1827 don fara aikin shari'a.[2]

Mutuwa da binnewa

[gyara sashe | gyara masomin]

James Semple ya mutu a Elsah a ranar 20 ga Disamba, 1866, kuma an binne shi a makabartar Bellefontaine a St. Louis.

A cikin 1819, Semple ya auri Ellen Duff Green, ƙanwar Duff Green.[2] Ta mutu a 1821, kuma a cikin 1833 Semple ya auri Mary Stevenson Mizner, 'yar ga Dr. Caldwell Cairns da Maryamu (Stevenson) Cairns, kuma bazawarar Henry Mizner.[2].

Agolan Semple, Lansing B. Mizner ɗan siyasan Amurka ne kuma jami'in diflomasiyya wanda ya yi aiki a matsayin Ministan Amurka a ƙasashen tsakiyar Amurka da dama.[2] Jikansa (daga agolan sa) Addison Mizner sanannen masanin gine-gine ne, kuma ɗayan jikansa Wilson Mizner sanannen marubucin wasan kwaikwayo ne.

Eugene Semple, ɗanɗan James da Mary Semple, ya yi aiki a matsayin Gwamnan yankin Washington daga 1887 zuwa 1889.[2] 'Yarsa Lucy Virginia ta zama matar attajiri daga St. Louis dan kasuwa Edgar Ames.[2] Bayan mutuwarsa, Lucy Ames ta faɗaɗa kasuwancin mijinta kuma ta ƙara yalwar dukiyarsa, kuma ta zama sananniya a matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasa ciki har da neman ayyuka ga mata da ilimi mai zurfi ga mata.[2] Diyarsa Julia ita ce matar Ashley D. Scott, wacce ta gudanar da kasuwancin siyar da kayan masarufi da tayi nasara a St. Louis kuma wacce ta kafa Mystic Order of Veiled Prophets of the Enchanted Realm ta kuma shirya Veiled Prophet Balll.[2]

Dokta Robert Semple, ɗan'uwan James Semple, shi ne wanda ya kafa Benicia, California, kuma shugaban babban taron tsarin mulki na California na 1849.[4]

  1. https://en.wikipedia.org/wiki/James_Semple#CITEREFEncyclopedia_of_American_Recessions_and_Depressions
  2. 2.00 2.01 2.02 2.03 2.04 2.05 2.06 2.07 2.08 2.09 2.10 2.11 2.12 2.13 2.14 2.15 2.16 Biography: General James Semple, pp. 62–74.
  3. 3.0 3.1 Encyclopedia of American Recessions and Depressions, p. 718
  4. "Robert Baylor Semple, Pioneer", pp. 130–131.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.