Jump to content

Isyaka Rabi'u

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Isyaka Rabi'u
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 1928
ƙasa Najeriya
Mutuwa Landan, 8 Mayu 2018
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u Malamin Addinin Musulunci ne, kuma shahararren ɗan kasuwa ne wanda ya daɗe yana ayyukan taimakawa al'umma da Addinin Musulunci ga dukan ƙungiyoyi a lokacin rayuwarsa. Wanda Shahararen ɗan kasuwa ne Wanda ake ma lakabi da BUA. [1][2]

An haifi marigayi Isyaku Rabi'u a shekara ta (1928 ) ga iyalan Muhammadu Rabi'u Ɗan Tinki, wanda mai wa'azin Addinin Musulunci ne daga Bichi cikin jihar Kano a Najeriya.

Daga shekara ta alif ɗari tara da talatin da shida (1936) zuwa shekara ta alif ɗari tara da arba'in da biyu (1942) marigayin ya halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur'ani da Larabci.

Daga nan ya tafi Maiduguri domin karo Ilimi, kuma bayan ya gama karatunsa a can ne ya dawo gida da niyyar yin aure.

Bayan yayi auren kuma ya tafi Zaria gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na'iya, inda ya samu shekaru biyu yana ɗalibta.

A shekarar alif ɗari tara da arba'in da tara (1949) ya kasance malamin Addini mai zaman kansa, inda yake koyar da Larabci da Alqur'ani ga ɗalibansa. Kuma a cikin daliban akwai Ibrahim Musa Gashash.

A farko shekarun (1950) Mallam Isyaku Rabi'u ya fara kasuwanci, duk da cewa bai bar koyarwa ba. Ya kafa wani kamfani mai suna Isyaku Rabiu & Sons a shekara ta(1952).

Da farko kamfanin ya fara da zama dilan kayan kamfanin UAC ne, wanda a wancan lokacin ke kasuwanci akan kekunan dinki, da litattafan Addinin Musulunci da kuma kekuna.

A shekara ta (1958), kamfanin ya sami bunƙasa bayan da aka kafa masakar Kaduna Textile Limited kuma kamfanin na Isyaku Rabiu & Sons ya zama daya daga cikin dilolinsa na farko.

Marigayin ya zama babban dilan kamfanin a arewacin Nashiiya, kuma a Shekara ta (1963 )shi da wasu 'yan kasuwa daga Kano suka hadu don kafa Kano Merchants Trading Company.

Wannan kamfanin ya jure wa gasa daga kamfanonin da ke shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Ya kuma kafa wani kamfani mai dinka kayan sawa a shekara ta (1970).

A lokacin da aka fara siyasar janmuriya ta biyu, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya goyi bayan jam'iyyar NPN wadda ta mulki kasar.

Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.

A shekarun (1970), kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.

A shekarar (1972 ), ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saƙa zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.

Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.

Amma saboda faduwar darajar Naira, kamfanin ya mayar da hankalinsa wajen kere-kere da kasuwanci kaya.

Marigayi Isyaku Rabi'u ya rasu ya bar mata da 'ya'ya har da jikoki masu yawa, kuma a cikin 'ya'yansa akwai Nafiu Rabiu, wanda shi ne babban dansa. Akwai kuma babban dan kasuwan nan, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA.[3]

Akwai kuma Rabi'u, mai kamfanin jirgin sama na IRS Airlines[4], da Naziru Rabi'u, da Quraish I Rabi'u, da Makiu Rabi'u, sai Abdullahi Rabi'u, da Muhammad Rabi'u, da Daha Rabi'u.

Kuma a fili yake cewa gidan marigayin na cikin gidaje mafi girma a duk fadin Kano.

Ayyukan sa domin taimaka ma al'uma

[gyara sashe | gyara masomin]

Ban da fagen karatun addini da kaswanci, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya yi fice wajen ayyukan taimako, wanda ya sa mutane da dama ke kaunarsa.

Malam Isyaka Rabi'u sanannen dan darikar Taijjaniyya ne, kuma yana daya daga cikin manyan almajiran shiek Ibrahim Nyass Kaulaha.

Abubuwan daya kamata a sani game da Isyaku Rabi'u
[gyara sashe | gyara masomin]

Wadannan su ne abubuwa guda bakwai da da wuya ka samu fahimtarsa:

1. Rabiu yazo duniya a ranar 9 ga Oktoba, 1928 cikin kungiyar Muhammadu Rabiu Dan Tinki da ke Bichi, Jihar Kano.

2. Mahaifinsa malamin addinin Islama ne wanda ya gudanar da nasa makarantar qurani.

3. Ya kaddamar da kungiyarsa mai suna Isyaku Rabiu da Yara a shekarar 1952.

4. Kungiyarsa ta samu yin musayar injinan dinki, litattafai masu tsattsauran ra'ayi da kekuna; daga baya kuma, kayan aiki.

5. Kamar dai lokacin da ya rasu Isyaku Rabi’u da ‘ya’yansa sun yi sha’awar harhadawa, kariya, banki da filaye.

6. Rabi’u ya kasance, har ya rasu, dan Tijjaniyya ne na gaba.

7. Isyaku Rabi’u mutum ne mai arziqi kuma mai bayar da gudunmawa[9

  1. Abdul-raheem, Hassan (15 May 2018). "Gudummawar Marigayi Khalifah Isyaka Rabi'u". dw.hausa.com. Retrieved 14 November 2021.
  2. "Kano billionaire, Isyaku Rabiu, is dead". premiumtimesng.com. 8 May 2018. Retrieved 14 November 2021.
  3. https://buagroup.com/management-team/
  4. https://en.wikipedia.org/wiki/IRS_Airlines