Bassey Asuquo
Bassey Asuquo | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Sunan asali | Bassey Asuquo |
Sunan haihuwa | Bassey Asuquo |
Yaren haihuwa | Harshen Ibibio |
Harsuna | Turanci, Hausa, Harshen Ibibio da Pidgin na Najeriya |
Writing language (en) | Turanci |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | Gwamnan jahar delta da Gwamnan jahar Edo |
Ilimi a | Kwalejin Hussey Warri |
Ƙabila | Mutanen Ibibio |
Eye color (en) | brown (en) |
Hair color (en) | black hair (en) |
Military or police rank (en) | Janar |
Mabiyi | Mohammed Abul-Salam Onuka |
Wanda ya biyo bayanshi | Baba Adamu Iyam (en) |
Personal pronoun (en) | L485 |
Bassey Asuquo sojan Najeriya ne wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban mulkin soja na jihar Delta tsakanin watan Disamban 1993 zuwa Satumban 1994, sannan kuma jihar Edo daga Satumban 1994 zuwa Disamban 1996, a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[1] Ya yi ritaya a matsayin Birgediya Janar.
A cikin shekarar 2008, ya kasance shugaban Clan na Anim Ankiong Clan Council na ƙaramar hukumar Odukpani a jihar Cross River. Ya shaida a gaban kwamitin majalisar da ke binciken kuɗaɗen wuta da ƙarafa da aka biya wa tashar samar da wutar lantarki ta Calabar 561MW GT, inda ya ce ƴan kwangila ne suka kawo tsaikon aikin ba wai turjiya daga al’umma ba.[2] A cikin watan Satumban 2009 an naɗa shi shugaban hukumar kula da masu taɓin hankali ta tarayyar Calabar.[3]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Ya halarci Hussey College Warri.[4]