Baiko
Appearance
Baiko | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | promise (en) da phase (en) |
Mabiyi | marriage proposal (en) |
Ta biyo baya | Aure, Aure da disengagement (en) |
Yana haddasa | fiancé (en) |
Hannun riga da | disengagement (en) |
Baiko, biki ne na yarjejeniya, akan amincewa da neman aure tsakanin namiji da mace.[1] A ƙasar Hausa kuwa, baiko wata al'ada ce wadda ake yi gabanin aure. Ana yin baiko ne a lokacin da Budurwa da Saurayi suka amince da cewa za su zauna da juna a matsayin ma'aurata. To a wannan lokacin ne za a dakatar da duk wani saurayi dake neman ta da aure, saboda cewa an amince za a aurar da ita ne ga wanda ta zaɓa daga cikin samarinta. Daga nan dangin ango za su kawo wa su kuɗi wanda ake kira da kuɗin baiko ko kuɗin sa rana tare da shaidu daga ɓangaren amarya da na ango. Bayan anyi baiko sai kuma shirye-shiryen ɗaurin aure.
Amma ga rayuwar Turawan kudancin duniya, sun ce baiko shi ne tsawon lokaci tsakanin sanarwar amincewa da neman aure.