Jump to content

Abdulla Yameen

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulla Yameen
President of the Maldives (en) Fassara

17 Nuwamba, 2013 - 17 Nuwamba, 2018
Mohammed Waheed Hassan (en) Fassara - Ibrahim Mohamed Solih (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Malé, 21 Mayu 1959 (65 shekaru)
ƙasa Maldives
Ƴan uwa
Ahali Maumoon Abdul Gayoom (en) Fassara
Karatu
Makaranta American University of Beirut (en) Fassara
Claremont Graduate University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Progressive Party of Maldives (en) Fassara
hoton abdullahi yameen
Abdullah Yameen
Abdulla Yameen

Abdulla Yameen Abdul Gayoom Da Harshen-dv|އަބްދުﷲ ޔާމީން އަބްދުލް ގައްޔޫމް larabci| عبد الله يامين عبد القيوم; An haife shi a ranar 21 ga watan Mayu, shekarar alif 1959, a jihar Malē dake kasar Maldives. Dan siyasar kasar Maldives ne, kuma shine Shugaba na 6th a kasar Maldives tun daga shekara ta 2013, yagaji Mohammed Waheed Hassan. inda yasake neman takara sake wani shekara biyar (5) a karo nabiyu.[1][2][3]

An zabi shugaba Yameen a zaben Kasar Maldives a shekara ta 2013, yayi takara karkashin jam'iyar Progressive Party (PPM), ya doke Shugaban jam'iyar Maldivian Democratic Party (MDP) kuma tsohon Shugaban kasar Mohamed Nasheed a zaben karo nabiyu bayan an kashe zaben da akayi da farko.[4] Yameen ne Shugaban kasar nabiyu da aka taba zaba karkashin tsarin mulkin Dimokaradiya a jamhoriyar Maldives.

Aiki kafin yazama Shugaba

[gyara sashe | gyara masomin]

Yameen yafara aikin gwamnati a watan July, shekarar alif 1978. Bayan karatun digiri dayayi a Beirut, Lebanon, yadawo gida a tsakiyar shekarar alif 1982, yafara aiki a matsayin Secretary a Department of Finance sannan yazama Research Officer a the Research and International Organisations Division of the Maldives Monetary Authority (MMA). Bayqn dawowarsa bayan yagama digiri na biyu, Yameen yafara aikin daya kaisa tsawon shekara ashirin (20) yanayi a Ministry of Trade and Industries. Daga cikin mukamai daya rike yayin aikinsa sune; Foreign Trade Development Officer, Undersecretary, Assistant Director, Deputy Director, Director, Director General and then the Minister of Trade and Industries a ranar 11 Ga watan November, shekara ta alif 1993.

A matsayin sa na Trade Minister, Yameen ya canja bangaren kasuwancin Maldives’ inda ya fadada tattalin arzikin kasar kuma ya kawo Karin saka jari a kasar Yameen yakasance daya daga cikin wadanda suka farfado da tattalin arzikin Maldives, bayan zamansa Dan kungiyar Multilateral Investment Guarantee Agency (MIGA) da wasu kungiyoyin kasuwanci na duniya.

Kasantuwarsa Minister of Trade and Industries (da kuma Minister of Trade, Industries and Labour), Yameen ya rike Minister of Higher Education, Employment and Social Security daga (watan July, shekarar 2005 zuwa watan April shekarar 2007) da kuma Minister of Tourism and Civil Aviation daga (watan Satumba shekarar 2008 zuwa watan Nuwamba shekarar 2008) a lokacin Shugaban cin Maumoon Abdul Gayoom.[5]

Shugabanci (2013 zuwa 2018)

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kwashe wasu tsirarun shekaru a jam'iyar People’s Alliance (PA), jam'iyar Siyasar da yataimaka aka kafa ta, Yameen yashiga jam'iyar Progressive Party of Maldives (PPM) a shekarar 2010. PPM itace jam'iyar tsohon Shugaban Kasar kuma dan'uwan Yameen wato Maumoon Abdul Gayoom, wanda ya mulki Kasar Maldives Tsawon shekaru 30. A zagayen farko da aka gudanar na Shugaban Kasar a shekarar 2013, tsohon Shugaban Kasar Mohamed Nasheed, wanda Yameen yake hamayya dashi yasamu 45.45% na yawan kuri'un da aka kada, shikuma Yameen yasamu kashi 25.35% na yawan kuri'un inda yakare a nabiyu, hakane yasa aka gudanar da zabe karo na biyu, sai Yameen Ya lashe zaben da kashi 51.39% na yawan kuri'un da aka kasa a zaben inda Nasheed yasamu kashi 48.61% kacal.


Huldar China-Maldives Friendship Bridge (wanda yanzu ake kira da Sinamalé Bridge) aiki, wanda aka soma a shekarar 2015, itace irinta ta farko a kasar Maldives. Tana da tsawon 1.4 kilometres da fadin 20 metres, tahada Malé karshen eastern zuwa kusurwan yammacin Hulhulé Island, inda tashar jirgin sama Velana take. Titin zai samar da hanya daya ne na tafiya wa ababen hawa hudu, da kuma hanya daya wa babura ako wace hanyar. Akwai hanyar masu tafiya a kafa suma ako wace bangaren hanyar.[6]

  1. cite web|url=https://www.aljazeera.com/news/asia/2013/11/maldives-swears-new-president-2013111711353221929.html%7Ctitle=Maldives[permanent dead link] swears in new president|last=|first=|date=|website=Al Jazeera|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=
  2. Cite web|url=https://www.bbc.co.uk/news/world-asia-24977601%7Ctitle=Yameen sworn in as president of the Maldives|last=|first=|date=|website=bbc.co.uk|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=}}
  3. Cite web|url=https://www.bbc.com/news/world-south-asia-12653773%7Ctitle=Maldives[permanent dead link] profile - Leaders|last=|first=|date=|website=BBC|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=
  4. Cite web|url=https://www.bbc.com/news/world-asia-24974019%7Ctitle=Maldives[permanent dead link] election: Abdulla Yameen wins run-off vote|last=|first=|date=|website=BBC|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=
  5. Cite web|url=https://presidency.gov.mv/president%7Ctitle=President[permanent dead link] Abdulla Yameen Abdul Gayoom|last=|first=|date=|website=presidency.gov.mv|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=
  6. Cite web|url=http://holidayplace.co.uk/news/details/118448/maldives-reveals-plans-for-airport-expansion-and-new-island-bridge%7Ctitle=Maldives[permanent dead link] reveals plans for airport expansion and new island bridge|last=|first=|date=|website=holidayplace.co.uk|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=