Charanchi
Appearance
Charanchi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 471 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Charanchi Karamar Hukuma ce da ke a Jihar Katsina, Arewa maso yammacin Nijeriya. Garin yana akan babbar hanyar Katsina zuwa Kano, shine Hedikwatar karamar hukumar. Garin yana akan lambar taswira 12°40'30''N.
Charanchi na da girman kasa kimanin 471km². Adadin yawan mutanen garin Charanchi 79,000 bisa kidaya ta 2006.
An kirkiri karamar hukumar Charanchi ne daga karamar hukumar Rimi a shekarar 1996.
Garin yana da jagorancin bangare biyu- yankin Charanci da Kuraye. Sarkin Shanun Katsina shine jagoran yankin Charanchi, shi kuma Sarkin kurayen Katsina ya na jagorantar yankin Kuraye.
Kauyukan garin Charanchi sun hada da:
Kuraye
Banye
Radda
Koda
Ganuwa
Yana
Sabon gari, da
Maje.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
.