Huang Huilin, mai shekaru 90, mamba ce ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wacce ta yi rayuwarta da kyau. A cikin shekarun 1950, Huang ta shiga cikin 'yan sa kai na jama'ar kasar Sin da suka shiga jamhuriyar dimokaradiyyar Koriya (DPRK) don taimakawa al’ummmar Koriya wajen yaki da maharan Amurka. Bayan ta dawo daga yakin kuma ta samu lambobin yabo na soja, ta yanke shawarar sadaukar da rayuwarta ga aikin koyarwa.
Usman Sa’id Sufi, dan kasuwan Najeriya ne da ya shigo birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, don halartar bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 7, ko kuma CIIE a takaice. A zantawarsa da Murtala Zhang, Usman Sa’id Sufi ya yi tsokaci kan muhimmancin bikin, da kuma abubuwan da ya kawo don baje-kolinsu a wannan karo, inda ya ce, manoman Najeriya za su ci gajiya sosai daga harkokin fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya, ciki har da kasar Sin.
A watan Mayun shekarar 2017 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a gun taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa na shawarar “ziri daya da hanya daya” cewa, kasar Sin za ta fara gudanar da baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE daga shekarar 2018. Shekaru shida a jere an gudanar da baje kolin CIIE cikin nasara, wanda ya kasance wani muhimmin mataki na dunkulewar tattalin arzikin duniya tare da bude kasuwannin kasar Sin ga duniya. Wannan ita ce
Kamfanin Joy Billiards na kasar Sin, wanda ke samar da teburan wasan kwallon Snooker, ya haskaka a yayin babban taron masu ruwa da tsaki na kasa da kasa a fannin wasan Snooker ko ANOC, wanda ya gudana a kasar Portugal, lokacin da kamfanin ya gabatar da nau’in wasan Snooker na “heyball” wanda a ake amfani da kwallayen Snooker 8 sabanin sauran nau’o’in wasan, ga shugabannin duniya masu ruwa da tsaki a harkar wasan, yana mai neman a shigar da nau’in Snooker na “heyball” cikin wasannin da za a rika yi yayin gasar Olympic.
Malam Mustapha Bulama, sanannen mai zanen barkwanci ne daga tarayyar Nijeriya, wanda mafi yawanci a kan ga zanensa a kafofin yada labarai da suka hada da Daily Trust da sauransu. A kwanakin baya, malam Mustapha Bulama ya kawo ziyara kasar Sin, musamman jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar.