Jihar Imo (Inyamurai: ra Imo), jiha ce dake Kudu maso Gabashin Najeriya. Ta hada iyaka daga gabas da Jihar Anambra, Jihar Rivers daga yamma da kudu, da kuma Jihar Abia daga gabas. Jihar ta samo asalin sunanta ne daga Kogin Imo wanda ke kwarara ta iyaka gabashin Jihar. Babban birnin jihar shi ne Owerri, kuma ana yi wa jihar lakabi da "Eastern Heartland" wato Cibiyar kasashen Gabas.

Imo


Suna saboda Kogin Imo
Wuri
Map
 5°29′N 7°02′E / 5.48°N 7.03°E / 5.48; 7.03
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Owerri
Yawan mutane
Faɗi 5,408,756 (2016)
• Yawan mutane 978.08 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 5,530 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Gabas ta Tsakiya
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Executive Council of Imo State (en) Fassara
Gangar majalisa Imo State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 460001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-IM
Wasu abun

Yanar gizo imostate.gov.ng
garin imo
tambarin gwamnatin imo


sashin shari'a na jami'ar imo
gate din jami'ar imo

Acikin jihohi talatin da shida 36, na Najeriya, Jihar Imo ita ce jiha ta uku mafi kankanta a Najeriya, kuma ita ce jiha ta sha hudu 14, a yawan jama'a da mutum akalla miliyan biyar da dugo hudu 5.4, dangane da kiyasin shekara ta dubu daya da sha shida 2016. Ta fuskar yanayin kasa kuwa, Jihar ta kasu kashi biyu dazukan Niger Delta swamp daga can kuryar gabashin jihar, sai kuma busassun dazukan Cross–Niger a sauran sassan jihar. Sauran muhimman Wurare sun hada da doramu da koguna kamar su Kogin Awbana, Kogin Imo, Orashi, da kuma Otamir tare da Tafkin Oguta a yammacin Jihar Imo.[1]

Jihar Imo ta yau na dauke da kabilu da dama, musamman Inyamurai tare da harshen Igbonci da kuma turanci a matsayin yarukan farko a jihar. Kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, yankin Jihar Imo ta yau na daga cikin yankin Masarautar Nri, sannan daga baya kuma Aro Confederacy kafin daga bisani Turawa su yake Jama'a Aro a wani ya da ake kira Yakin Anglo-Aro. Bayan yakin, turawa sun hade yankin acikin Yankin Kudancin Najeriya wacce daga baya ta zamo Najeriya ta Burtaniya a shekarar dubu daya da dari tara da sha hudu 1914; bayan an hade yankin kuma, Jihar Imo ta zamo cibiyar adawa da mulkin turawa a Yakin Mata.

Bayan samun 'yancin Najeriya, yankin Jihar Imo ta yau na daga cikin Yankin Gabashin Najeriya har zuwa shekarar dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967, lokacin da aka raba yankin kuma ta fada Karkashin Jihar Gabas ta Tsakiya. Kasa da watan in biyu bayan hakan, tsohuwar Yankin Gabashin Najeriya ta janyo yakin basasa wanda aka kwashe tsawon shekaru uku ana gwabzawa tsakanin Gwamnatin Najeriya da kuma yankin Biyafara. An yi musayar wuta sosai a yankin musamman a Owerri har zuwa lokacin da aka ba Owerri babban birnin Biyafara a shekarar dubu daya da dari tara da sittin da tara 1969. Sojojin Najeriya sun kame yankin Imo ta yau a shekarar dubu daya da dari tara da saba'in 1970, a yayin da aka gudanar da wani farmaki mai suna Operation Tail-Wind aka mamaye yankin kuma aka kawo ka

Karshen yakin. Bayan yaki ya Kare, kuma an sake hade yankin acikin Najeriya, Imo ta koma karkashin Yankin Gabas ta Tsakiya, har zuwa shekarar dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976, lokacin da aka ba ta jiha a lokacin mulkin Murtala Mohammed.[2] Shekaru goma sha biyar bayan hakan, an raba Jihar Imo inda gabashinta ta zamo Jihar Abiya.[3][4]

Tattalin arzikin jihar kuwa sun ta'allaka ne akan noma da kiwo, musamman noman kwakwan manja wanda mutane da dama sun dogara dashi a wajen girki. Muhimman masana'antu sun hada da sarrafa man fetur da kuma gas, musamman a yankunan arewaci da kuma yammacin Jihar Imo. Jihar ta yi fama da rikice-rikice iri-iri a lokuta daban daban na tarihin jihar, daga cikin wadanda suka yi fice sun hada rikicin magance sihirce-sihirce wato Rikicin Otokoto na 1996, da kuma rikicin da ake yi a yanzu haka na Eastern Security Network da dai sauransu. Duk da rikicin da ke faruwa a yankin, Jihar na fuskantar cigaba ta fuskar yawan jama'a da kuma masana'antu, Imo itace ta shida Jerin Jihohi Najeriya dangane da Ma'aunin Cigaban dan Adam.

Tana da yawan filin kasa kimanin kilomita arabba’i 5,530, da yawan jama’a miliyan uku da dubu dari tara da talatin da hudu da dari takwas da tisa'in da tara (kidayar yawan jama'a shekara dubu biyu da shida 2006). Babban birnin Jihar itace Owerri. Kuma Rochas Okorocha shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Prince Eze Madumere. Dattawan jihar sun hada da: Samuel Anyanwu, Hope Uzodinma da Benjamin Uwajumogu.

cikin birnin imo
Shagulgulan imo

Jihar Imo ta hada iyaka da Jihar Abiya daga gabas, Rive Niger da Jihar Delta daga yamma, Jihar Anambra daga arewa sai kuma Jihar Rivers daga kudu. Jihar tana da lambobin wuri kamar haka; lattitude 4°45'N da 7°15'N, sai kuma longitude 6°50'E da 7°25'E, tare da kasa mai girman 5,100, sq km.

Albarkatun kasa.

gyara sashe

Jihar tana da albarkatun kasa kamar man fetur, gas, lead, calcium carbonate, wuta mai amfani da hasken rana da mai amfani da iska, da kuma zinc. Muhimman tsirrai su hada da icen iroko, mahogany, obeche, bamboo, bishiyar roba da kuma icen kwakan manja. Bugu da kari akwai tabo, yashi da kuma farar kasa a jihar Imo

Harkokin man fetur da gas.

gyara sashe

Akwai rijiyoyin man fetur guda dari da sittin da uku 163, a yankuna daban daban guda sha biyu 12, a jihar.

Kananan Hukumomi.

gyara sashe

Jihar Imo nada adadin Kananan hukumomi guda ashirin da bakwai (27). Sune:

Manazarta.

gyara sashe
  1. "What are the two lakes in Imo State?". big board scouting. 22 July 2022. Retrieved 3 September 2022.
  2. "History of Imo State | Culture | Economy | People | Naijabiography". Naijabiography Media. Retrieved 3 September2022.
  3. "This is how the 36 states were created". Pulse.ng. 24 October 2017. Retrieved 15 December 2021.
  4. "Abia | state, Nigeria | Britannica". www.britannica.com. Retrieved 12 March 2022.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara